Recent Posts

LightBlog

Breaking

LightBlog

Friday, October 19, 2018

⚜⚜ LABARIN FATIMA⚜⚜

Sosae Babana ya rikice gani yakeyima kaman nima mutuwan zanyi tashi yayi ya dauko ruwa ya yayyafa min amma shiru kakeji ko motsi banyi ba.... Duk irin jarum takar da yake dashi saida kwalla suka zuba a idanunsa, Yana cikin wannan halinne mama tashigo ta tarar dashi, gani a kwance shikuma yana zaune se kwalla da yaketa gangarowa a kuma tunsa a rikice mama ta isa gareni ta dagani ta daurani akan cinyarta tafara min fifita tana min addu'o'i tana tofamin cikin ikon Allah kuwa sai Na fara bude idanuna a hankali cikin nutsuwa Na fara kallon baba sai abubuwan da suka faru suka fara dawomin sabo, Kukane ya kwacemin kuka nakeyi tare da ambaton sunan Allah a bakina ....yanxu shiken suntafi kenan sun barni har abada bazan qara ganinsu ba Allah sarki ni Ashe dama baxanga dawowanku ba Allah ya jikanku ummina,Abba Na Allah ya gafarta muku yakai haske kabarinku yasa chan yafi muku nan da ameen suka amsamin baba tashi yayi yafita sabida bazai iya jure ci gaba da ganin irin kukan da nakeyiba Safiyace ta shigo ta kama hannuna muka koma dakinmu ,,' Dama rayuwa haka take yau kaine gobe baka nan kuma kowata rai dole za ta dandani mutuwa Allah INA toqonka kajiqan wa'anda suka rasu ka gafarta musu muma intamu tazo kasa mucika da kyau da imani...!AMEEN"" Akwana tashi babu wahala yau kwanan abbana arba'in kenan da rasuwa duk da babu abinda Na rasa a gidan amma kullum iyayena suna raina kuma bana gajiya dayi musu addu'a Assalamu alaikum wae ana sallama da Fatima a waje Fatima kuma inji mama kenan, eh Fatima inji wani a waje yaron yasake maimaitawa a karo Na biyu Sosae maganan ya doki mama ta fara tunani Fatima kuma? Tashi tayi tashiga dakin su fatiman tasameta a kwance da azkar a hannunta tana karantawa bataji shigowan Maman ba saiji tayi ta dafata tace Fatima wanine a waje yake kiranki... Juyowa nayi nace mama ni kuma..?? Naqara da cewa kodae safiya ake nema...? Girgixa minkai tayi tace A'ah Fatima akace ba safiya ba amma tashi kije ki gani Da toh Na amsa mata, tashi nayi Na dauki hijab domin xuwa ganin me kiran.. Tunani mama tashiga yi to wae yama za a ayi ace ana sallama da Fatima bayan safiya CE 'yar gida Kenan haka Na nufin Fatima zata riga safiya samun miji kaii baxai sa6uba da sake Idan har Fatima akace za a fara aurar wa kenan Baban safiya kudi ze kashe babu adadi Dan kuwa naga tun bayan rasuwar iyayan yarinyar nan sae wani jawota jikinsa yakeyi shiga 'yar d'an Uwa Amma bari dae taje ta dawo inji tun wuri insan abinyi Dan gaskia babu yanda za ayi haka ta faru ina da rai da lafia ehe..... Haka mama tayita sak'esak'e aranta shedan kuma yana qara ingixata, Tunda Na fito Na hango wani a zaune akan mashin bangane ko wayeba saida Na matso dab dashi naga Ashe malamin islamiyyan mu ne Malam isa Sallama nayi masa ya dago yana kallona Na gaishesa ya amsamin still idonsa akaina sainaji duk Na takura Shiru naji yayi saena Dan dago fiskata domin inga me yakeyi saenaga har yanxu kallona yakeyi Na bud'e baki xanyi magana sae naji yace Fatima Zarah ya hakuri nace masa Alhamdulillah..! Cigaba yayi dayimin nasihohi dakuma qara jaddadamin akan inci gaba da hakuri, godia nayi masa sosae saboda dukna qagara inkoma cikin gida Dan ni banta6a tsayuwa da wani awaja ba sai yau. Fatima.... Na'am Na amsa tare da juyowa,,, Na tsayar dake duk kin gaji ko?? Nace masa um, Kimin magana mana inji please,, Sunkuyar dakaina nayi nace dama inaso inshiga cikine kar aga Na Dade... Yanxu zaki tafi amma inason inyi wata muhimmiyar magana dake ne ko inbari sae gobe ne indawo ?? A'ah ka gayamin yanxu kawae Dan ba acika son muna fitaba Toh Fatima azahirin gaskia dae tun ba yanxuba Allah ya jarabceni da sonki sai yau Allah ya bani ikon Sanar miki, fatima ki temaka min karkice min a'ah... Saboda ina burin kizamo mahaifiya ga 'ya 'yana.., Wani irin ajiyan zuciya Na sauke, saae abin yazomin wani kala, tunanin Abbana yadawomin sabo har idona yacika da kwalla... Abbana yana cemin Fatimanah duk ranar da wani yace yana sonki to kafin ki amince masa ki fara turasa waje Na kinji ko,, Da eh Na amsa masa..... Sai gashi ranar tazo amma abbana baya raye sosae na yi jarumta wajan 6oye hawayan da suke qoqarin saukomin dan kuwa idona harya kad'a yayi ja.. Idonsa akaina yace kiyi hak'uri inna 6atamiki rai girgiza masa kai nayi nace masa nikam babu abinda zance amma kafara zuwa kanemi izini wajan abbana, duk abinda yace ayi insha Allah haka za ayi.... Murmushi yayi yana mejin dadin kalamaina, Sallama namasa nashiga cikin gida shikuma ya hau mashin dinsa yatafi A tsakar gida Na tarar da mama, kirana tayi tace Fatima zo nan naje Na samu gefanta Na zauna nace gani...! Saiji nayi tace wayazo gunki kuma me yazo yi... ?? Sai nace mata..

No comments:

Post a Comment