Recent Posts

LightBlog

Breaking

LightBlog

Friday, October 19, 2018

BUDURWAN SIRRI

Washe gari da safiya naje na iske mahaifina a turakarsa domin jin abunda ya samu daga istaharan da yayi , Da sallamata na shiga cikin turakar na sameshi a zaune a wajen dana iskeshi jiya, Ya dago kai daga kallon kasa dayakeyi yana mai amsa sallamata, Na samu waje na zauna, Mahaifina yayi gyaran murya sannan ya fara bayani "haseena hakika Allah ba azzalumin bawansa bane, Jiya nayi istahara domin neman zabin Allah akan wannan mugun al'amari dayake tunkaro mu, An nuna mani a mafarkina cewa wani Dan Adam ne kadai zai iya tseratar da mu daga sharrin sarki Rava, dolenmu muje duniyar mutane mu dauko wani yaro wanda bansan sunansa ba, sannan zamu dukufa wajen sana'anta wata makami wacce ba'ataba yin irinta ba a doron kasa, da taimakon wannan makami ne zamu samu nasaran murkushe Garin Bulzum, an nuna mani dukkan wani abun da zamu bukata wajen sana'anta wannan makami a cikin mafarkina, " Yayi shiru yana mai dubana domin jin abunda zance Cikin doki nace "toh Abba waye wannan shi Dan Adam din da zai kubutar damu " "Bansan ko waye ba amma an nuna mani alomin da zan iya ganeshi, kuma kece da kanki zaki futa nemansa," Cikin tantama nace mai "toh amma Abba da wasu alamomine zan iya gane sa, ?" "Alama na farko shine a lokacin da kuka hadu da shi hadari zai hadu, kuma zaiyi hatsari a babur har ya karye a kafansa na dama, a lama na biyu shine yana da makaken tabo a tafin hannunsa na dama, wayannan sune alamomin da zaki iya ganeshi da su, " , Daga nan mahaifina ya tsara mani dukkan wani shiri da kuma tsari na yadda zanyi na daukoka daga duniyarku, harda irin shirin da zamu shirya maka" Haseena tayi shiru tana dubana a lokacin da mamaki da Al'ajabi suka dabaibayeni, nama rasa tacewa Haseena ta cigaba "Inhar bazaka mantaba shuraih akwai wani lokacin da ka taba yin hatsari har ka karye a kafarka ta dama, tun daga wannan lokacin na lura da tabon dake tafin hannunka, wannan yasa na daukoka tundaga duniyarku na kawoka nan dun ka taimakemu , shi kansa SALMAN shirine muka hada amma babu wani burbushin soyayya a tsakaninmu , " Sai ayanzu na gane dukkan manofofi da inda maganar haseena BUDURWAN SIRRI ya nufa iyayena,abokaina,kasata,mahaifana duk na rabu da su akan mace guda wacce a tunanina tana Sona da gaskiyane, tabbas na kamu da kaunarta irin kaunar da bazan iyya rayuwa imbabu ita ba, Irin kaunar da zan iya sadaukar da duk abun dana mallaka don ita Irin kaunar da zan iya bayar da rayuwata don ceto nata amma ashe ita ba kaunata take ba, Bansan lokacin da kwalla suka fara zarya akan kumatuna ba, haseena ta budi baki da niyyar ta sake furta wata kalma Cikin gaggawa na daga mata hannu alaman bana son sake jin wata magana daga bakinta na tashi tsaye fuskata ta sauya lokaci guda numfashina ya fara fita da sauri, zuciyata na tafasa nace da ita "Babu komai haseena NAJI NA GANI zan taimaki Al'ummanku da duk wata taimako da kuka nema daga wajena, amman bai kamata ......" Sai kuma nai shiru ga barin maganar duk da naso na furta wata magana amma na fasa kwalla ne suka kara gangarowa daga idanuwana , Na lura da haseena sai kallona takeyi tana son tai mani magana amma ganin irin yanayin dana ke ciki yasa taja bakinta tai gum . Jiki ba kwari ta fice daga dakin, Wani tsatsauran ciwon kaine ya fara ziyartar kwalkwata , na dafe kaina ina mai runtse idanuwa , babu abun da idanuwana suke hango mani face kyakkyawan suran nan na haseena , madaidaicin bakinta wanda baya rabo da murmushi , suke ta zarya a cikin kwalkwata, . A haka bacci yai awon gaba dani Bani da farkawa ba sai cikin dare koda na tashi na bude kofa na fice daga dakina, iyanzu kam na gane cewa haseena ba kaunata take ba, na gane cewa haseena ba sona take ba duk wasu abubuwa da suka wanzu a baya duk yaudarace don na biya mata bukatarta, nai murmushin takaici bisa ganin irin wasa da hankalina da tunanina da haseena tayi , Na mike wata hanya wacce zata sadani da babban falon fadan, cikin yan mintuna na isa falon kaman yadda na zata hakan take Al'umman aljanu ne cikin shigar mutane suna ta harkokinsu, na nufi wata kofa na bude Hasken rana yai wa idanuna maraba, Na fice daga falon na nufi farfajiyan masarautan ina mai kallon irin salon da akai amfani da shi wajen ginin gidan, Kai tsaye babbar kofar fita daga Gidan na nufa bansha wahala ba wajen tuhuma ta da masu gadi sukai, daga baya suka bani hanya na fice daga gidan sarautar gaba daya, Ni kaina bansan me ya futo dani ba kuma bansan dalilin fitana ba ni dai na tsinci kaina ina mai Tafiya nake ina mamakin irin ginin gidajen Garin, kwata kwata tsawon ginin bazai wuce kamu goma ba , kuma da zallar zinare suka sana'anta gidajen, Gaba dayan gidajen suna kamanceceniya da juna Sa'I sa'I nakan cimma jama'a suna harkokinsu baki kawai nake saki ina kallonsu duk daya kasance Aljanu ne amma ba zaka taba iya banabacesu da mutane ba , Ina cikin tafiya ban aune ba sai jin wata kakkausar murya nayi ta kwala mani kira Shakka babu na taba jin wannan murya, na juyo don ganin mai kiran nawa Salman ne na gani yana falfala a zabababben gudu a bayansa akwai wasu askarawa su hudu dukkansu suna masu falfala gudu don cimmini Cikim yam dakikoki suka iso gabana salman ya dubeni murmushi dauke a kan fuskarsa yace "Shuraih! Fitarka daga masarauta yana da hatsari sosai, don kuwa akowane lokaci sarki rava zai iya kawo ma ziyara don ya dade da jin labarinka" ************************************** . Ina zaune a gaban mahaifin haseena kaina ya na kallon kasa , yan majalisan sarki suna kewaye da shi kaman kullum "Shuraih kai hakuri bisa rabaka da mukayi da iyayenka da kasarku, sannan muna rokonka daka taimakemu daga masifan dake tunkararmu" Maganganunsa ne suka sanya na dago kaina ina mai dubansa, acikin zuciyata nace toh waishin ni da ban kwarance wajen fada ba tayaya har zan iya taimakonsu, "Nasan kana mamaki da jin cewa da mukai kaine zaka iya taimakonmu ka tserartar damu daga halaka da iznin Allah SWT" Salman ya fadi sannan yaci gaba "kamar yadda budurwan sirri tai maka bayani, ajiyane muka karashe aikin sana'anta wata makami wacce ba'ataba sana'anta makamanciyarta ba a doron kasa, wannan makamin tamkar nakiya take saide ita tana aikine kawai akan jinsin Aljanu , Gobe da safe zakaayi shiri mu baka wannan makami ka nufi garin Bulzum ka dasa ta " , ******** Shuraih ! Shuraih !! Shuraih!!! Muryan mahaifiyata na tsinkaya da sauri na futo daga cikin dakina na A tsaye na taras da ita a kofan dakin "Kazo wata ce tazo wajenka" "Toh mama" Amsar dana iya bata kenan Na mike na nufi kofan dakina Turus nayi ina kallonta murmushin dake fisgo zuciyata gareta dauke a kan lebbanta, "Haseena !" Firgigit na farka daga nannauyan baccin dayai awon gaba dani dazu, nan take dukkan abubuwan da suka faru dani suka fara dawowa cikin kwalkwata sai ayanzu naji ina matukar kewan gida, na tuna da mahaifiyata inna mairo, "Kwab kwab kwab" Karan bugun kofa ya katse mani tunanina , Na tashi naje na bude kofan Tsaye a gabana cikin kayan daana saba ganinsa , Fuskarsa sai murmushi take tamkar wanda aka mai kyautan Aljanna, "Kayi sauri ka shirya, maimartaba na nemanka " "Toh "kawai na iya cewa Cikin yan mintuna nai wanka na shirya cikin wasu kayan dana taras da su akan katifa , Nayi mamaki ainun da ganin kayan, bakin suite ne mai dauke da dan ciki, hade da wando damamme , ' ******* Zaune nake a gaban maimartaba , salman yana gefen damana yayinda haseena take gefen haguna,

No comments:

Post a Comment